Isa ga babban shafi

Haaland ya lashe kyautar gwarzon Firimiyar Ingila

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Erling Haaland, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar Firimiyar Ingala ta bana.

Erling Haaland dan wasan Manchester City na murnar lashe gasar Firimiyar Ingila.
Erling Haaland dan wasan Manchester City na murnar lashe gasar Firimiyar Ingila. AP - Jon Super
Talla

Haaland da ya samu nasarar zura kwallaye 36 a gasar ta wannan kaka, lamarin da ya bashi damar hawa kan ‘yan wasa 7 wajen samun nasarar lashe zabe daga wajen kyaftin din kungiyoyi 20 da suka fafata a gasar, da kuma na kwamitin kwararru na masu kulada harkar kwallon kafa a kasar.

‘Yan wasan da suka fafata wajen lashe kyautar sun hada da abokin wasan sa Kevin De Bruyne da dan wasan Arsenal Bukayo Saka da Harry Kane da Martin Odegaard da Marcus Rashford sai kuma Kieran Trippier.

Haaland ya zama dan wasan kungiyar Manchester City na 4 da ya lashe wannan kyauta, ganin yadda a baya Kevin De Bruyne ya taba lashe ta a kakar shekarar 2019/2020 da kuma 2021/2022, akwai kuma Ruben Dias da ya lashe a 2020/2021 sai Vincent Kompany da ya fara lashewa a kungiyar a kakar shekarar 2011/2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.