Isa ga babban shafi

Manchester City ta lashe kofin FA na 7

Manchester City ta samu nasarar lashe gasar kofin FA ta bana, bayan jefa kwallaye biyu da dan wasan ta Ilkay Gundogan ya yi a ragar Manchester United a wasan karshe da su ka ta shi 2-1 a Asabar din nan.

Mai horas da kungiyar kwallon kafar Manchester City, Pep Guardiola, da wasu 'yan wasan kungiyar bayan lallasa Manchester United a wasan karshen FA. 03 Yuni 2023.
Mai horas da kungiyar kwallon kafar Manchester City, Pep Guardiola, da wasu 'yan wasan kungiyar bayan lallasa Manchester United a wasan karshen FA. 03 Yuni 2023. REUTERS - CARL RECINE
Talla

A yanzu dai City za ta maida hankali ne wajen lashe wasan karshe da za ta yi da Inter Milan a ranar Asabar mai zuwa, don taddo tarihin da United ta taba kafarawa na zamowa kungiyar kasar Ingila ta farko da ta lashe manyan kofuna uku na Firimiya da FA da kuma na zakarun Turai na kakar shekarar 1998/1999.

Gundogan ya ci kwallo ta farko ne a dakika 12 da fara wasan, wacce ta zamo kwallo mafi Sauri da aka taba jefawa a wasan karshe na gasar.

Wasan da ya gudana a filin wasa na Wembley wanda kuma shine na farko da kungiyoyin biyu suka taba hadu a wasan karshe na gasar kofin FA, ya samu halartar mutane 83, kuma shine karo na 7 da kungiyar ta taba lashewa a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.