Isa ga babban shafi

Ibrahimovic ya yi ritaya bayan lashe kofuna 34 a manyan kungiyoyin Turai 6

Zlatan Ibrahimovic ya yi ritaya daga kwalllon kafa, matakin da ya sanar a ranar Lahadin nan da ta gabata, bayan wasan karshe na kakar wasa ta bana da kungiyarsa ta AC Milan ta buga.

Zlatan Ibrahimovic yayin bankwana da kungiyar AC Milan bayan yin ritaya daga kwallon kafa.
Zlatan Ibrahimovic yayin bankwana da kungiyar AC Milan bayan yin ritaya daga kwallon kafa. © AC MILAN
Talla

Yayin wasan na gasar Seria A, AC Milan ce ta lallasa Verona da 3-1 a filin wasanta na San Siro, inda a nan ne Ibrahimovic ya ce lokaci ya yi na bankwana da buga kwallon kafa baki daya.

Dan wasan dai na daga cikin ‘yan gaba da suka fi yin fice wajen mallakar basirar sarrafa kwallon kafa tamkar masu sihiri a duniyar tamaula, abinda ya sa shi zama daga cikin mafi kwarewa da aka taba gani a tarihin kwalllon kafa.

Zlatan Ibrahimovic yayin wasan karshe na kungiyar AC Milan a kakar wasa ta bana. 4 Yunin, 2023.
Zlatan Ibrahimovic yayin wasan karshe na kungiyar AC Milan a kakar wasa ta bana. 4 Yunin, 2023. AFP - GABRIEL BOUYS

Ibrahimovic mai shekaru 41 a yanzu, ya lashe kofuna 34, da kuma cin kwallaye 570 a matakan kungiyoyi da na tawagar kasarsa, a tsawon lokacin da ya shafe yana haskawa a fagen kwallon kafa.

A kungiyar Malmo FF a kasar ta Sweden cikin shekarar 1999 dan wasan ya fara buga wasa a matakin kwararru, bayan shekaru biyu kuma ya kulla yarjejeniya da Ajax, daga nan ne kumma ya koma Juventus, sai Inter Milan, kana Barccelona a shekarar 2009.

Daga Spain Ibrahimovic ya sake komawa Italliya, inda ya kulla yarjejeniya da AC Milan daga bisani kuma ya koma PSG a shekarar 2012.

Ragowar kungiyoyin da Ibrahimovic ya buga wa wasanni sun hada da Manchester United da LA Galaxy ta Amurka, kafin ya sake komawa AC Milan inda nan ne yayi ritaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.