Isa ga babban shafi

Hukumar wasannin Spain ta hukunta wadanda suka ci zarafin Vinicius

Hukumar wasannin kasar Spain ta hukunta mutane bakwai da ta samu da laifin cin zarafin dan wasan Real Madrid Vinicius Junior ta hanyar nuna masa wariyar launin fata, nuna masa kyama a matsayinsa na bako, da kuma yi masa barazana.

Dan wasan Real Madrid Vinicius Junior yayin nuna bacin rai akan cin zarafin nuna wariyar launin fata da aka  yi masa, a lokacin waasan da suka buga da kungiyar Valancia. 21 ga Mayu, 2023.
Dan wasan Real Madrid Vinicius Junior yayin nuna bacin rai akan cin zarafin nuna wariyar launin fata da aka yi masa, a lokacin waasan da suka buga da kungiyar Valancia. 21 ga Mayu, 2023. AFP - JOSE JORDAN
Talla

A karkashin hukuncin, an yanka wa maza hudu daga cikin masu laifin biyan tarar Euro dubu 60, sai kuma haramta musu shiga filayen wasanni da tsawon shekaru biyu, bayan samunsu da laifin rataye wani rubutun batanci ga Vinicius a harabar filin wasan da Real Madrid da kara da Atletico Madrid a ranar 26 ga watan Janairun da ya gabata.

Ragowar masu laifin uku kuwa, an ci su tarar Euro dubu 5,000 kowannensu, tare da dakatar da su, daga halartar filayen wasanni tsawon shekara guda, bayan samunsu da laifin furtawa da kuma yin alamun nuna wariyar launi ga Vinicius Junior yayin karawar Real Madrid da Valencia a ranar 21 ga Mayu.

Tuni dai masu ruwa da tsaki da sauran fitattun mutane suka mara wad an wasan mai shekaru 22 baya kan neman hukunta wadanda suka ci zarafin na sa, yayin da gwamnatin kasar sa ta Brazil ta bukaci daukar tsauraran matakai akan duk wanda aka samu da laifin nuna wariyar launi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.