Isa ga babban shafi

Kasashe 14 sun samu tikitin zuwa gasar AFCON na 2023 a Cote d'Ivoire

Kasashe 14 daga cikin 24 sun samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 da Cote d’Ivoire zata karbi bakwanci, bayan kammala wasannin sharan fage na biyar a karshen mako.

Dan wasan Najeriya da Saliyo yayin wasan neman gurbin shiga kasar neman cin kofin Afirka a Laberia.18/06/23.
Dan wasan Najeriya da Saliyo yayin wasan neman gurbin shiga kasar neman cin kofin Afirka a Laberia.18/06/23. © CAF
Talla

Tuni tawagar Super Eagles ta Najeriya da Guinea-Bissau suka samu tikiti a rukunin A, sai kuam Cape Verde a rukunin B da kuma Mali daga rukunin G bayan wasan da suka doka a karshen mako.

Sauran kasashe da suka samu gurbin shiga gasar ta AFCON akwai Ivory Coast mai masaukin baki da Senegal da Algeria da Burkina Faso da Masar da Equatorial Guinea da Morocco da Afirka ta Kudu da Tunisia da kuma Zambia.

Akwai sauran wasanni uku da za a buga ranar Talata don kammala zagaye na biyar na wasannin neman cancanta.

Tuni kasashen Sao Tome et Principe, Botswana da Lesotho da Madagascar da Libya da Laberiya da Comoros da Sudan ta Kudu da kuma Habasha suka rasa damar samun gurbi a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.