Isa ga babban shafi

Kante ya bi Benzema zuwa Al-Ittihad na Saudiya

Dan wasan tsakiya na Chelsea da Faransa N'Golo Kante ya amince ya kulla yarjejeniya da zakarun Saudiya Al-Ittihad.

Ngolo Kante na Faransa  yayin sarrafa kwallon a wasan rukunin C tsakanin Faransa da Peru a gasar cin kofin duniya ta 2018. 21 ga Yuni, 2018 (AP Photo/David Vincent)
Ngolo Kante na Faransa yayin sarrafa kwallon a wasan rukunin C tsakanin Faransa da Peru a gasar cin kofin duniya ta 2018. 21 ga Yuni, 2018 (AP Photo/David Vincent) AP - David Vincent
Talla

A karshen watan Yunin nan ne kwantiragin dan wasan mai shekaru 32 zai kawo karshe a Stamford Bridge.

N’Golo Kante ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku da kungiyar kan kudi fam miliyan 86.

Wasanni tara kacal Kante ya buga wa Chelsea a kakar 2022-23 da aka karkare saboda fama da rauni.

Zai hadu da Karim Benzema

Zai hadu da Karim Benzema a Al-Ittihad bayan da dan kasarsa Faransa ya bar Real Madrid kuma ya koma Saudiya a kwantiragin shekaru uku.

Ana iya kwantanta Kante amatsayin wanda ya samu nasarori a sabgar kwallon kafa ta Ingila.

Ya taka rawar gani a Ingila

Ya taimakawa Leicester City lashe gasar Premier a kakar wasa ta 2015 -16 kafin ya koma Stamford Bridge. A Chelsea Kante ya lashe gasar zakarun Turai, Premier League, Europa League da kuma gasar cin kofin FA.

An ba shi kyautar Gwarzon dan wasa na kungiyar marubata labarin wasanin Ƙwallon kafa a kakar 2016-17.

Kofin duniya

Ya kuma taka rawar gani yayin da Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya a 2018.

Da wannan mataki Kante zai hade da Benzema da wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar Cristiano Ronaldo a gasar Saudiyya.

An danganta manyan ‘yan wasa da dama da za su koma daya daga cikin manyan kasashen Saudiyya. Yayin da Lionnel Messi ya ki amincewa da tayin Saudiya ya koma Inter Miami a farkon wannan watan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.