Isa ga babban shafi

Harry Kane ya nuna sha'awar komawa Bayern Munich

Dan wasan gaba na Tottenham, Harry Kane, mai shekaru 29 ya nuna sha’awar komawa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar Jamus kamar yadda  rahotannni ke nunawa, sai dai abin Bayern din ta taya shi kan kudi Fam miliyan 60 ne kawai, abin da mahukuntan kungiyarsa ke ganin ya yi kadan ainun.

Harry Kane, dan wasan gaba na Tottenham da Ingila.
Harry Kane, dan wasan gaba na Tottenham da Ingila. REUTERS - ANNEGRET HILSE
Talla

Tottenham tana so ta sayar da dan wasan gabanta ne a kan kudi Fam miliyan 100, kuma ga shi dan  wasan bai nuna alamun sake rattaba hannu a wata sabuwar yarjejeniya ba, duk kuwa da cewa kwantiraginsa zai kare a kaka mai zuwa.

 Halin rashin tabbas da ya dabaibaye batun sabanta kwantiragin Kane na iya  kara wa Bayern Munich damar sayen daan wasan, saboda yana iya zama silar tilasta shugaban Tottenham, David Levy yin la’akari da sallama shi a kan farashin da ya yi kasa da wanda ya yyi niyyar sayar da shi, duk da cewa yana matukar bukatar ci gaba da zama da dan wasan a arewacin birnin Landan.

Majiyoyi dai sun ci gaba da zakewa cewar Tottenham za ta sa kafa ta yi  fatali da duk wani yunkuri  da wata kungiya za ta yin a sayen Kane a wannan kaka, kuma abin jira a gani shine ko Bayern Munich za ta biya wannan kudi da ya kai Fam miliyan 100.

Kungiyoyi da suka hada daa Manchester United da Real Madrid duk sun nuna bukatar dauko wannan dan wasa, sai dai babu wani haske a lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.