Isa ga babban shafi

Inter Miami ta gabatar da Lionel Messi gaban dubban magoya baya

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami ta gabatar da sabon dan wasanta na gaba Lionel Messi gaban dandazon magoya baya a filin wasa na DRV PNK a daren jiya lahadi.

Lionel Messi yayin gabatar da shi gaban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami.
Lionel Messi yayin gabatar da shi gaban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami. AP - Rebecca Blackwell
Talla

Magoya baya fiye da dubu 20 suka yi dandazo don tarbar Messi na Argentina mai shekaru 36, galibi sanye da rigar dan wasan mai lamba 10.

Messi wanda ya lashewa kasar sa kofin Duniya a Qatar cikin shekarar da ta gabata, ya gabatar da jawabin godiya cikin harshen sipaniyanci gaban magoya bayan.

Bikin tarbar Lionel Messi.
Bikin tarbar Lionel Messi. AP - Marta Lavandier

A karshen wannan kaka ne Messi mai shekaru 36 da ya lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or har sau 7 ya amince da komawa Inter Miami don taka leda karkashin gasar ta MLS bayan karewar kwantiraginsa da PSG ta Faransa.

A jawabinsa Messi ya sha alwashin bayar da gudunmawa kamar yadda ya bayar a duk inda ya taka leda.

Sabon kwantiragin Messi da zai kai shi nan da shekarar 2025, zai ba shi damar hadewa da tsohon abokin wasansa Sergio Busquet da shi ma ya rabu da Barcelona a watannin baya zuwa kungiyar ta Inter Miami, Wanda shi ma aka gabatar da shi a jiyan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.