Isa ga babban shafi

Manchester United na gab da kamma cinikin Onana daga Inter Milan

Da yiwuwar cinikin da Manchester United ke kishirwar yi na gab da kammaluwa wato dai kan mai tsaron raga Andrea Onana da manaja Erik ten Hag ya kwallafa rai aka.

Mai tsaron ragar Kamaru da ke taka leda da Inter Milan André Onana.
Mai tsaron ragar Kamaru da ke taka leda da Inter Milan André Onana. REUTERS - ALBERTO LINGRIA
Talla

Wasu majiyoyi sun ce an yi ganawa tsakanin wakilan Onana da United a jiya lahadi inda aka cimma jituwar cinikin matashin mai tsaron ragar kan yuro miliyan 50 a kwantiragin shekaru 5 da zabin karin wa’adi.

Onana dan Kamaru mai shekaru 27 da zai maye gurbin David De Gea da ya rabu da kungiyar a makon jiya bayan shafe shekaru 12, majiyoyi sun ce da yiwuwar United za ta yi amfani da shi hatta a wasannin tunkarar sabuwar kaka da za ta doka a Amurka cikin makon nan.  

Manaja ten Hag wanda ya ce yafi gamsuwa da salon wasan Onana fiye da de Gea wanda ya gaza sauya zuwa zubin da shi Hag ke bukata, ya ce ya yi imanin Onana zai zama mai tsaron ragar da kungiyar ke mafarkin samu.

Onana dai ya yi wasa karkashin manaja ten Hag yayin zamansa a Ajax da ya shafe shekaru 7 gabanin komawa Inter Milan bara, inda aka gaza zura masa kwallo a wasanni 8 cikin 24 da ya doka karkashin Serie A.

Idan har wannan ciniki ya tabbata, Onana zai zama dan wasa na biyu da United ta saya cikin wannan kaka bayan Mason Mount daga Chelsea kan yuro miliyan 55.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.