Isa ga babban shafi

Manchester United ta tube Harry Maguire daga mukamin kyaftin

Harry Maguire ya rasa mukaminsa na Kyaftin a tawagar kwallon kafa ta Manchester United bayan sauye-sauyen manaja Erik ten hag ya bi kansa.

Mai tsaeon baya na Manchester United Harry Maguire.
Mai tsaeon baya na Manchester United Harry Maguire. POOL/AFP
Talla

Mai tsaron bayan na Ingila mai shekaru 30 da United ta sayo daga Leicester City kan yuro miliyan 80 a watan Janairun 2020, ya rasa gurbinsa na haskawa a kowanne wasa karkashin manajan wanda ke ci gaba da sauye-sauye a cikin tawagar.

Sanarwar da United ta fitar ta ce Ten Hag zai bayyana sabon kyaftin din kungiyar kowanne lokaci gabanin balaguron tawagar zuwa New York a alhamis din makon nan.

Maguire wanda Ole Gunna Solsha ya nada kyaftin watanni 5 bayan zuwansa kungiyar, a kakar da ta gabata wasanni firimiya 8 kacal aka faro da shi yayinda wasu jita-jita ke alakanta shi da komawa West Ham United duk da yadda yak e da saura a kwantiraginsa har zuwa nan da shekarar 2025.

A cewar Maguire tabbas bai ji dadin hukuncin na Ten Hag ba amma hakan ba zai hana shi ci gaba da bayar da gudunmawarsa ga kungiyar ba, tare da alfahari da magoya baya.

Sanarwar tube Kyaftin Maguire, ta godewa dan wasan da irin gudunmawar da ya bayar a tsawon lokacin da ya dauka yana wannan jagoranci.

Maguire wanda ya haska a wasanni 31 cikin 62 da United ta doka a dukkan gasa rike da mukamin na kyaftin sau da dama Bruno Fernandes ke rike mukamin wajen jagorantar tawagar idan baya nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.