Isa ga babban shafi

Ronaldo ne aka fi biyan kudi masu yawa a manhajar Instagram

Dan wasan kungiyar kwallon kafar Al-Nassr Cristiano Ronaldo, ya zama mutumin da manhajar sadarwar zamani ta Instagram ta fi biyanshi da tsada a duk wata talla da ta sanya a shafinsa.

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Portugal Cristiano Ronaldo.
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Portugal Cristiano Ronaldo. TT NEWS AGENCY/AFP
Talla

Ronaldo mai shekaru 38, a yanzu ana biyan shi kudin da ya kai Yuro miliyan daya da dubu dari 8 da 70 a duk wata talla da aka saka a shafinsa, wanda hakan yasa ya sha gaban ‘yar Amurka Kylie Jenner, wadda ke samun Yuro miliyan daya da dubu dari 4 da 70.

Tsohon dan wasan na Real Madrid da Manchester United, na da mabiya shafinsa na Instagram da suka kai miliyan dari biyar da dubu dari 9 da 70, ya yinda Kylie ke da mabiya miliyan dari 3 da dubu dari 9 da 70.

Lionel Messi ne ke a mataki na uku, inda ake biyansa kudin da suka kai Yuro miliyan daya da dubu dari 380.

A ‘yan shekarun nan dai, Cristiano ya samu gagarumin tagomashi a shafin na Instagram, domin a shekarar 2019 mataki na 3 ya ke, inda ake biyansa kudin da ya kai Yuro dubu dari 755.

Cristiano ya samu tagomashin ne bayan bayyana shi a matsayin dan wasan da aka fi biya da tsada a duniya, inda ya ke daukar kudin da ya kai Yuro miliyan dari da 9 a duk shekara.

A watan Janairun da ya gaba ne Ronaldo ya kowa gasar Saudi Pro ta kasar Saudiya, lamarin da ya bashi zama dan wasan da yafi amsar albashi a karon farko tun shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.