Isa ga babban shafi

'Yan wasa 3,000 daga kasashe kusan 30 zasu halarci wasannin Francophonie a DRCongo

Yayin da ya rage mako guda a soma wasar kasashe  masu amfani da harshen Faransanci da aka sani da Francophonie , ma’aikata a birnin Kinshasa na iya kokarinsu wajen kammala aiki gabanin gasar .

Daya daga cikin filayen wasannin kwallon kafa da za a  gudanar da wasannin Francophonie
Daya daga cikin filayen wasannin kwallon kafa da za a gudanar da wasannin Francophonie © GUERCHOM NDEBO / AFP
Talla

Kimanin 'yan wasa 3,000 daga kasashe kusan 30 ne ke shirin isa babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a cikin 'yan kwanaki masu zuwa gabanin fara wasan na ranar 28 ga watan Yuli.

Duk da haka, an fara atisayen biki a filin wasa na Stade des Martyrs.

Wasannin Francophonie
Wasannin Francophonie © D.R.

An zaɓi DRCongo a 2019 a matsayin mai masaukin baki na wasannin Francophonie karo 9, taron da ake gudanarwa duk shekara huɗu wanda ya haɗa duka wasanni da al'adu.

Tun da farko dai an shirya gudanar da wasannin ne a shekarar 2021, amma an dage gasar saboda cutar amai da gudawa da aka sani da Cholera, sannan kuma an sake jinkirta wasannin a bara saboda ba a shirya kayan aikin ba.

Ministan harkokin wajen DRCongo Christophe Lutundula ya shaidawa manema labarai ranar Alhamis cewa hada kudi domin daukar nauyin gasar wasanni ta kasa da kasa abu ne mai wahala musaman wannan lokacin da muke cikin yaki.

Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun addabi mafi yawan gabashin kasar, wanda ya barke tun shekarun 1990 da 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.