Isa ga babban shafi

Har yanzu babu tabbas kan makomar Mbappe duk da tayin da Al Hilal ta yi masa

Kokarin kafa tarihin kashe makudan kudade wajen kulla yarjejeniya da dan wasa guda da kungiyar Al Hilal ta gasar Saudiya ke yi, na cigaba da daukar hankalin masu ruwa da tsaki a fagen wasanni musamman kwallon kafa. 

Kylian Mbappé
Kylian Mbappé REUTERS - STEPHANIE LECOCQ
Talla

A farkon makon nan ne dai Al Hilal ta mika wa PSG tayin biyan euro miliyan 300 domn kulla yarjejeniya da dan wasanta Kylian Mbappe a daidai lokacin da dangantaka ke kara yin rauni a tsakanin kungiyar da tauraron dan wasan na ta, biyo bayan kin tsawaita yarjejeniyarsa da yayi, wadda za ta kare a shekarar badi ta 2024. 

Kafin tayin da Al Hilal ta gabatar dai, Real Madrid ce ke kan gaba tsakanin manyan kungiyoyin da ke neman kulla yarjejeniya da Mbappe, duk da cewar ya ki karbar tayinta a kakar wasan da ta gabata. 

Ya zuwa yanzu kungiyoyin da suka bayyana aniyarsu ta neman kulla yarjejeniya da Mbappe sun hada da Al Hilal, da Real Madrid, da Manchester United, da Inter Milan, da Barcelona sai kuma Tottenham. 

Sai dai har yanzu dan wasan bai fito karara ya bayyana inda ya karkata ba, yayin da ya dage kan cewa lallai yana son kammala yarjejeniyarsa da PSG, wadda za ta kare a kakar wasa ta 2024.

Dan wasan na Faransa mai shekaru 24 ne ke rike da tarihin zura kwallaye mafi yawa a PSG, inda ya ci wa kungiyar kwallaye 212 a cikin wasanni 260. 

Har yanzu kuma Mbappe ne dan wasa na biyu mafi tsada a duniyar tamaula bayan takwaransa na PSG Neymar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.