Isa ga babban shafi

Zaha ya sauya sheka zuwa gasar kwallon kafar Turkiya daga Ingila

Tauraron Crystal Palace Wilfred Zaha ya sauya sheka zuwa Galatasaray bayan karewar yarjejeniyar da ke tsakaninsa da tsohuwar kungiyarsa. 

Wilfried Zaha
Wilfried Zaha POOL/AFP
Talla

 

A halin yanzu dan wasan zai rikar karbar albashin euro miliyan 4 da kusan rabi ne duk shekara a sabuwar kungiyar ta sa da ke kasar Turkiya, inda ake sa ran zai shafe shekaru uku yana haska wa. 

Kafin sauyin shekar da yayi dai, Zaha ya shafe shekaru masu yawa a Crystal Palace, kungiyar da ya kulla yarjejeniya da ita tun yana da shekaru 12, inda ya buga mata wasanni 458, tare da ci mata kwallaye 90. 

Daga cikin jerin bajintar da ya nuna a tsohuwar kungiyar tasa akwai taimaka wa Cruystal Palace da yayi wajen komawa Firimiyar Ingila daga gasar Championship mai daraja ta biyu a shekarar 2013, bayan da a shekarar 2010 ya fara buga mata wasa a matakin kwararru. 

A baya dai an sha alakanta Zaha da Shirin sauyin sheka zuwa kungiyar Arsenal ko kuma daya daga cikin kungiyoyin da ke gasar kwallon kafar Saudiya, wadda a yanzu haka take cigaba da kokarin nannado kwararrun ‘yan wasa daga nahiyar Turai. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.