Isa ga babban shafi

Faransa ta kawo karshen mafarkin Morocco a gasar cin kofin duniya

Faransa ta kawo karshen mafarkin Morocco, wato kungiyar da ta fito daga nahiyar Afirka, ta sha kashi a hannun abokiyar karawarta a gasar cin kofin duniya ta mata.

Tawagar Faransa kenan, lokacin da suke murnar doke Morocco a gasar cin kofin duniya ta mata.
Tawagar Faransa kenan, lokacin da suke murnar doke Morocco a gasar cin kofin duniya ta mata. REUTERS - CARL RECINE
Talla

Kwallayen da Kadidiatou Diani da Kenza Dali da kuma Le Sommer suka zura a ragar Marocco ne suka bawa tawagar Faransa kwarin gwiwa, wato sun samu 3-0 kafin a tafi hutun rabin lokaci, daga bisani kuma Le Sommer ta kara ta biyu bayan mintuna 70, wato bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kenan.

Yanzu Faransa za ta kara da Australia a zagayen ‘yan takwas wato dab da na kusa da na karshe, a Brisbane ranar Asabar.

Morocco ta yi fatan zama ta farko a Afirka da za ta yi nasara a gasar cin kofin duniya ta mata.

Mafi kyawun sakamakon da Faransa ta samu a wasan karshe na gasar cin kofin duniya shi ne na hudu da ta kasance a shekarar 2011, kuma a yanzu ta kai matakin ‘yan takwas a wannan gasa.

Yayin da aka fitar da kasashe 10 na farko wato Amurka da Jamus da Brazil da kuma Canada, a yanzu Faransa na fatan lashe wannan gasa.

Morocco kasa ta farko daga yankin Larabawa kuma daga Afirka da ta fafata a wasan karshe a gasar ta mata, ta yi nasarar zama ta biyu a rukunin H wato ta sha gaban Jamus wadda ta lashe gasar har sau biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.