Isa ga babban shafi

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Spain ya shiga uku bayan sumbatar wata 'yar wasa

Firaministan Spain Pedro Sanchez ya caccaki shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta kasar, Luis Rubiales kan yadda ya sumbaci 'yar wasan da ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya ta mata, Jenni Hermoso. 

 Luis Rubiales,shugaban hukumr kwallon kafar Spain.
Luis Rubiales,shugaban hukumr kwallon kafar Spain. Reuters
Talla

A cewar firaministan, bayar da hakuri kan lamarin kawai ba zai isa ba idan aka yi la'akari da girmar abin da ya faru. 

Hotunan bidiyon da suka yadu sun nuna yadda Rubiales ya kama tare da sumbatar Hermoso a lebe a kan mumbari yayin bikin gabatar da kofin gasar cin kofin duniya ta mata da suka lashe a karon farko, ranar Lahadin da ta gabata bayan da Spain ta doke Ingila da ci 1-0. 

A nata bangaren, ‘yar wasan da aka sumbata wato Hermoso, ta ce ko shakka babu ba ji dadin abin da shugaban Hukumar Kwalllon Kafar ya yi mata ba, amma ta ce hakan ba wani abin damuwa ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.