Isa ga babban shafi

FIFA ta fara binciken shugaban hukumar kwallon kafar kasar Spain Rubiales

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta bude shari'ar ladabtarwa kan shugaban hukumar kwallon kafa ta Spain Luis Rubiales saboda wani abu mai kama da rashin da’a da ya nuna a wasan karshe na cin kofin duniya na mata.

Luis Rubiales lokacin da yake sumbatar 'yar wasan Spain, bayan lashe gasar cin kofin duniya ta mata da FIFA ta shirya.
Luis Rubiales lokacin da yake sumbatar 'yar wasan Spain, bayan lashe gasar cin kofin duniya ta mata da FIFA ta shirya. © Captura de tela imagens France24
Talla

Rubiales ya sumbaci ‘yar wasan gaba Jenni Hermoso a lebe bayan Spain ta doke Ingila.

Rahotanni daga kasar Spain sun bayyana cewa Rubiales na shirin yin murabus daga mukaminsa ranar Juma'a kuma tuni ya sanar da abokan aikinsa matakin nasa.

Kwararru a bangaren tamola na ganin cewa, Rubiales ya rasa goyon bayan ’yan wasa, da gwamnati, da Fifa, da ma kungiyoyin wasanni da suka dogara da kasafin kudin tarayya ko kuma gwamnati.

FIFA za ta duba ko abin da ya aikata ya kasance karya doka ta 13 a cikin ka'idojin ladabtarwar ta, game da nuna dabi’un da basu kamata ba.

Hukumar ta nanata kudurinta na mutunta 'yancin kowa da kowa kuma ta yi kakkausar suka ga duk wani hali sabanin haka, in ji sanarwar.

A bisa ka'idar ladabtarwa, jami'ai na daga cikin wadanda dole ne su bi ka'idojin wasa, aminci da rikon amana.

Hukumar da ke kula da harkokin kwallon kafa a duniya, ta ce za a iya daukar matakan ladabtarwa ga duk wanda ya saba ka'idojin da'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.