Isa ga babban shafi

Nunez ya zura kwallaye 2 a wasan da Liverpool ta doke Newcastle har gida

Darwin Nunez ya zama tauraron Liverpool da ya kai tawagar ga nasara a karawarta da Newcastle United, duk da yadda kungiyar ta karkare karawar ta jiya da ‘yan wasa 10 bayan dankarawa kyaftin dinta Virgil van Dijk jan kati tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci.

Dan wasan gaba na Liverpool Darwin Núñez da ta sayo daga Benfica.
Dan wasan gaba na Liverpool Darwin Núñez da ta sayo daga Benfica. © LUSA - JOSÉ SENA GOULÃO
Talla

Wasan wanda ya gudana a gidan Newcastle United wato filin wasa na St James Park tun da fari Anthony Gordon ya zura wa bakin kwallon farko a minti na 25 bayan kuskuren da Trent Alexandre-Arnold ya yi a gab da ragar Liverpool amma kuma cikin kasa da mintuna 3 Nunez ya farke wato a minti na 28 kuma a hakane a aka tafi hutun rabin lokaci.

Gab da farke kwallon da Nunez ya yi ne kuma van Dijk ya yiwa Alexandre Isak wata keta wadda ta kai ga korar shi daga fili, lamarin da ya zama babban kalubale ga tawagar ta Jurgen Klopp.

Yayin wasan na jiya Alisson Becker ya yi rawar gani wajen barar da tarin kwallayen da ‘yan wasan na Newcastle suka rika kai farmaki ciki har da wadda Miguel Amiron ya shammace amma kuma ba ta kai ga nasara ba.

'Yan wasan Liverpool yayin murnar samun nasara.
'Yan wasan Liverpool yayin murnar samun nasara. AP - Rui Vieira

Ana gab da karkare wasa a minti na 81 ne Liverpool ta zura kwallonta na biyu wadda Nunez din ya sake zura da taimakon Mohamed Salah.

Nasarar ta Darwin Nunez da Liverpool ta saya kan fam miliyan 85 a kakar da ta gabata, na iya kawo karshen caccakar da dan wasan ke sha saboda rashin katabus duk da makuden kudaden da aka sanya wajen sayenshi.

A kakar da ta gabata cikin wasanni 42 da ya doka Nunes dan Uruguay mai shekaru 24 kwallaye 15 kacal ya iya zurawa yayinda ya rasa damarmaki har 28 da ake ganin zai iya amfani da su wajen zura kwallo, lamarin da ya haddasa masa kakkausar suka musamman biyo bayan koma bayan da kungiyar ta gani.

Yanzu haka dai Liverpool wadda ta rasa damar zuwa gasar cin kofin zakarun Turai ta na a matsayin na 4 ne a teburin na Firimiya bayan canjaras a biyu cikin wasanni 3 da ta doka ta kuma lashe guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.