Isa ga babban shafi
Wasanni

Ozil ya kama hanyar zama shugaban tawagar kwallon kafar Turkiya

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon dan wasan Arsenal da Real Madrid Mesut Ozil na shirin zama sabon shugaban kungiyar kwallon kafar kasar Turkiyya.

Tsohon dan wasan Jamus Mesut Ozil yay hira da manema labaru a Turkiya
Tsohon dan wasan Jamus Mesut Ozil yay hira da manema labaru a Turkiya AP
Talla

Rahotanni sun ce hukumar kwallon kafar Turkiyya na shirin korar kocinta Stefan Kuntz da babban manajan kungiyar Hamit Altintop.

Kungiyar ta musanta cewa ta na shirin koran Kuntz, amma a wata sanarwa da ta fitar ta tabbatar da cewa Bajamushen zai halarci wani taro da su ranar Laraba.

Turkiya ta kama hanyar zuwa gasar Turai

A halin yanzu Turkiyya ce ta biyu a rukuninta na neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2024, kuma tana da tabbacin samun gurbi, amma ta sha kashi a hannun Japan da ci 4-2 a wasan sada zumunci a lokacin hutu.

Tsohon dan wasan Jamus Mesut Ozil yayin atisaye a Turkiya
Tsohon dan wasan Jamus Mesut Ozil yayin atisaye a Turkiya © Ozil twaitter

An kuma bayar da rahoton cewa Kuntz ya samu sabani da fitaccen dan wasan tsakiya na Turkiya Hakan Calhanoglou.

A cewar jaridar Bild na Jamus, makomar Altintop a matsayin babban manajan ita ma na fuskantar barazana, inda fitaccen dan wasan Turkiyya ke zama kashin bayar nadin Kuntz.

Ana kallon tsohon kocin Jamus Joachim Low a matsayin wanda zai iya maye gurbin Kuntz, inda rahotanni suka ce Ozil ya shiga jerin wadanda zasu iya maye gurbin Altintop.

Tsohon dan wasan Jamus Mesut Ozil
Tsohon dan wasan Jamus Mesut Ozil AP

Ozil ya taka leda a karkashin Low har zuwa lokacin da ya rataya takalmar sa a Jamus, inda ya zura kwallaye 23 a wasanni 92 da ya buga wa kasar tsakanin 2009 zuwa 2018.

Dan wasan tsakiya ya kasance babban dan wasa a gasar cin kofin duniya karkashin Joachim Low a shekarar 2014.

Ritayar Ozil

Ozil ya sanar da yin ritaya daga buga wasan kwallon kafa na kasa da kasa bayan gasar cin kofin duniya ta FIFA a 2018 bayan an nuna masa wariyar launin fata da rashin mutuntawa.

Dan wasan tsakiyar da abokin wasansa Ilkay Gundogan, wanda dan asalin kasar Turkiyya ne, sun tayar da hankula a Jamus bayan da aka nuna hotonsu tare da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a jajibirin gasar cin kofin duniya ta 2018.

Cece-kuce

Ozil ya fuskanci suka sosai kan hotonsa da Erdogan, wanda masu sukarsa suka bayyana a matsayin dan kama-karya na zamani, sannan ziyarar kwanaki uku da ya kai Landan a shekarar 2018 ya fuskanci zanga-zanga daga kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama.

A baya dai Ozil ya kare matakin da ya dauka na ganawa da shugaban kasar tare da daukar hoton da suka yi yayin da yake mika masa rigar Arsenal da ta sa hannu. Bayan shekara guda Erdogan ya kasance babban bako a bikin auren Ozil da matarsa Amine Gulse.

Idan Ozil ya zama magajin Altintop a matsayin babban manaja, hakan zai nuna saurin dawowa kwallon kafa ga tsakiya.

A watan Maris ne ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa, bayan da ya yi fama da rauni a Istanbul Basaksehir.

Ozil ya koma kungiyar ne daga Fenerbahce bayan kawo karshen kwantiraginsa da Arsenal a shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.