Isa ga babban shafi

Rashford na Manchester United ya yi hadarin mota bayan nasararsu a kan Burnley

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ya yi hadarin mota bayan dawowa daga wasan da suka yi nasara kan Burnley da kwallo 1 mai ban haushi karkashin gasar Firimiyar Ingila.

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford.
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford. AFP/File
Talla

Hadarin ya faru ne lokacin da Rashford mai shekaru 25 ya bar sansanin atisayen Manchester United na Carrington a cikin farar motar sa kirar Rolls Royce.

Bisa al’ada, babbar motar kungiyar kan ajje ilahirin ‘yan wasan na Manchester United ne a filin atisayen na Carrington bayan kwaso su daga duk kungiyar da suka buga wasa da ita, inda daga nan kuma kowanne dan wasa zai dauki motarsa don tafiya gida.

Wasu hotunan bayan faruwar hadarin sun nuna yadda motar ta Rashford ta daddauje ko da ya ke bayanai sun ce ya na cikin koshin lafiya.

Rashford na Ingila na cikin tawagar Erik Ten Hag da suka doka ilahirin mintuna 90 na wasan da suka yi nasara kan Burnley da kwallo 1 mai ban haushi.

Wannan nasara dai ta kawo karshen rashin nasara a wasanni 3 a jere da Manchester United ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.