Isa ga babban shafi

'Yar tseren Habasha Tigist Assefa ta lashe gasar tseren Duniya a birnin Berlin

‘Yar tseren Habasha Tigist Assefa ta yi nasarar lashe gasar tseren duniya da ke gudana a birnin Berlin na Jamus bangaren mata bayan da ta kammala zagayen karshe na gudun kilomita 10 a sa’o’i 2 da mintuna 11 da dakika 53, kasa da mintuna 2 idan an kwatanta da nasararta ta bara.

'Yar tseren Habasha Tigist Assefa da ta zo ta daya a gasar tseren Duniya da ta gudana a birnin Berlin na Jamus.
'Yar tseren Habasha Tigist Assefa da ta zo ta daya a gasar tseren Duniya da ta gudana a birnin Berlin na Jamus. REUTERS - LISI NIESNER
Talla

Wannan nasara ta Assefa mai shekaru 29 ta goge tarihin nasarar Brigid Kosgei na Kenya da ya kafa tarihin kammala makamancin tseren a sa’o’i 2 da mintuna 14 da dakika 4 yayin gasar tseren duniya da ta gudana a birnin Chicago na Amurka cikin shekarar 2019.

Assefa ta yi nasarar kammala zagayen karshe na tseren na ta ne da tazarar mintuna 5 da dakika 56 tsakaninta da Sheila Chepkirui ta Kenya da ta zo ta biyu kana mintuna 6 da dakika 48 tsakaninta da Magdalena Shauri ta Tanzania da ta zo ta 3.

Nasarar ta Assefa na nuna cewa ita ce mace ta farko da ta kafa makamancin wannan tarihi bayan Naolo Takahashi ta Japan a shekarar 2001.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.