Isa ga babban shafi

An samun karuwar adadin magoya bayan kwallon kafa da ake cafkewa a Birtaniya

Adadin shekarun da aka dauka ana kama mutanen da ke yiwa doka karan tsaye a filayen wasannin kwallon kafa a Ingila da Wales ya kai shekaru tara, a cewar alkaluman ma'aikatar cikin gida.

Magoya bayan Liverpool da ke tsaye a wajen filin wasa, yayin da suka gaza samun damar shiga domin kallon wasan da kungiyar ta fafata da Real Madrid PSG a gasar zakarun Turai da ya gudana a filin wasa na Stade de France a Saint-Denis, Gabashin birnin Paris, ranar 28 ga watan Mayu, 2022.
Magoya bayan Liverpool da ke tsaye a wajen filin wasa, yayin da suka gaza samun damar shiga domin kallon wasan da kungiyar ta fafata da Real Madrid PSG a gasar zakarun Turai da ya gudana a filin wasa na Stade de France a Saint-Denis, Gabashin birnin Paris, ranar 28 ga watan Mayu, 2022. AFP - THOMAS COEX
Talla

An kama mutane 2,264 masu alaka da keta dokar kwallon kafa a tsakanin shekarar 2022-23, adadi mafi yawa tun 2013-14 da kuma karuwar 66 a kakar wasan da ta gabata.

Kame a wasannin mata, da aka yi a Ingila da Wales a wasannin kasashen ketare, da kuma kame kan mallakar kwayoyin na cikin alkaluman da aka fitar a karon farko.

A kakar wasa ta 2022-23, mutum 200 aka cafke da muggan kwayoyi yayin da aka kama 101 a Ingila da Wales a kokarinsu na halartar gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar.

Ko da yake babu wanda aka kama a gasar cin kofin duniya ta mata da ta gudana.

An bayar da sabbin umarnin dakatar da wasan kwallon kafa har guda 682 a kakar wasan da ta gabata, wanda ya karu da kashi 32 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2021-22, kuma shi ne adadi mafi girma da aka bayar tun 960 da aka samu a kakar wasa ta 2010-11.

Daga cikin umarnin dakatarwa 1,624 da aka ayyana a ranar 1 ga Agusta 2023, maza 1,618, kuma1,133 daga cikinsu basu wuce tsakanin shekaru 18 zuwa 34.

Magoya bayan Manchester United 69 aka haramtawa halartar filin wasa, yayin da Millwall ke matsayi na biyu da adadi 66.

West Ham ce dai ke da yawan adadin mutum 89 na magoya bayan da aka kama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.