Isa ga babban shafi

Kofin US Open ya kufcewa Inter Miami bayan shan kaye a hannun Houston

Inter Miami ta yi rashin nasara da kwallo 1 da 2 a hannun Houston Dynamo yayin wasan karshe na cin kofin US Open da ya gudana jiya Alhamis.

Messi bai samu damar taka leda a wasan ba saboda famin tsohon rauni.
Messi bai samu damar taka leda a wasan ba saboda famin tsohon rauni. REUTERS - MARCO BELLO
Talla

Miami ta yi wasan ba tare da zakaranta Lionel Messi ba, wanda rauni ya tilasta cire daga wasansu da Orlando City a Litinin din da ta gabata.

Tun kafin wasan na ranar Litinin dama anga yadda Inter Miami ta yi amfani da Messi a matsayin sauyi yayin wasan ta da Toronto FC a makon jiya, sakamakon famin tsohon rauni da dan wasan na gaba ya yi.

Kwallayen Griffin Dorsey da Amine Bassi ne suka bai wa Houston nasara tun a zagayen farko gabanin Josef Martinez ya zurawa Inter Miami kwallo a gab da tashi daga wasan wanda ya gudana a filin wasa na Fort Lauderdale da ke Florida.

Mai tsaron ragar Houston Andrew Tarbell ya tare kwallayen ‘yan wasan Inter Miami har guda 3 da suka kusa shiga raga lamarin da ya bai wa kungiyar damar lashe kofin karo na 2 cikin shekaru 5.

Baya ga Messi shi ma Jordi Alba bai doka wasan na karshe ba saboda raunin da ya samu.

Kakar gasar ta lig din Amurka na karewa ne a ranar 21 ga watan Oktoba sai kuma doka wasannin cike gurbi a tsakanin ranakun 21 ga watan zuwa 9 ga watan Disamba.

Tun bayan komawarsa Inter Miami a watan Yulin da ya gabata daga PSG, Messi wanda ya lashe kofin duniya ya yi nasarar zuwa kwallaye 11 tare da taimakawa a zura wasu 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.