Isa ga babban shafi

Bellingham ya zura kwallo biyu a El- Clasico na farko da ya buga a gasar La Liga

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Jude Bellingham, ya zurawa Barcelona kwallaye biyu a raga, a wasan El- Clasico na farko da ya buka a gasar La Liga, lamarinda ya baiwa kungiyarsa nasara da ci 2-1.

Alokacin da dan wasan Real Madrid Jude Bellingham, ya zura kwallonsa ta farko a ragar Barcelona.
Alokacin da dan wasan Real Madrid Jude Bellingham, ya zura kwallonsa ta farko a ragar Barcelona. © france24
Talla

Dan wasan na Ingila, wanda ya fara taka leda a Madrid da zura kwallo a raga, ya farke kwallon da Ilkay Gundogan ya zura musu a filin wasan Barcelona na Olympics.

Daga nan Bellingham ya zura kwallo ta biyu ana dab da tashi daga wasan, wanda hakan ya sanya magoya bayan Barcelona yin shiru, wanda kuma ya sanya yawan kwallayen da ya ciwa Madrid a gasar La Liga a kakar wasan bana suka kai 10.

Kwallaye biyu da Bellingham ya ciwa Madrid ya sanya ta komawa matsayi na daya a teburin gasar La Liga, amma ban-bancin kwallaye ne tsakaninta da Girona da ke matsayi na biyu, sannan suka baiwa Barcelona tazarar maki 4.

Dan wasan Real Madrid, Jude Bellingham.
Dan wasan Real Madrid, Jude Bellingham. © AFP - PIERRE-PHILIPPE MARCOU

Mai horas da kungiyar Real Madrid Carlo Ancelotti bayan tashi daga wasan, ya ce akwai abin mamaki yadda dan wasan ya zura kwallon farko.

Duk da dawo daga jinyar rauni da ‘yan wasa irinsu Robert Lewandowski da Jules Kounde da Raphinha suka yi, mai horas da kungiyar Barcelona Xavi a benci ya barsu, sai dai har yanzu​​ Frenkie de Jong da Pedri ba su kammala murmure wa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.