Isa ga babban shafi
GASAR FIRIMIYA

Bournemouth ta lallasa Manchester United a 'Old Trafford'

Duniya – Kungiyar Bournemouth ta je har Old Trafford inda ta lallasa Manchester United da ci 3 – 0 a gasar firimiya, nasarar da ta dada fito da irin matsalolin da suka addabi kungiyar a kakar bana.

Andre Onana, mai tsaron gidan Manchester United
Andre Onana, mai tsaron gidan Manchester United AFP - OLI SCARFF
Talla

Wannan rashin nasara ta dada jefa shakku a kan makomar Manchester wadda a baya ta zama gagara gasa a ciki da wajen Ingila, lokacin da Sir Alex Ferguson ya jagorance ta.

Dominic Solanke ya fara jefawa Bournemouth kwallonta ta farko a mintuna 5 da fara wasa, abinda ya taimake su tafiya hutun rabin lokaci suna da ci 1 – 0.

Bayan dawowa daga hutu, Philip Billing ya jefawa Bournemouth kwallonta na 2 a mituna 68, yayin da Marcos Senesi ya jefa ta 3 a mintuna 73.

Kafin tashi a wasan Bournemouth ta jefa kwallo na 4 a ragar Manchester, amma sai alkalin wasa ya kashe bayan an gano cewar kwallon ta taba hannun ‘dan wasan gaba na bakin.

Wannan gagarumar nasara ta taimakawa Bournemouth dada ficewa daga kasan tebur, inda yanzu take mataki na 13 da maki 19, yayin da Manchester ke rike da matsayi na 6 da maki 27.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.