Isa ga babban shafi

Chelsea ta haye wasan kusa da karshe na kofin Carabao

Chelsea ta yi nasarar zuwa wasan kusa da na karshe na kofin Carabao bayan doke Newcastle 4-2 a bugun fanariti, bayan da aka tashi wasa 1-1 da yammaci Talata.

'Yan wasan Chelsea sun rungumi mai tsaron gidan Djordje Petrovic bayan ya ceci bugun daga kai sai mai tsaron gida Chelsea ta lashe wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Carabao. 19/12/23
'Yan wasan Chelsea sun rungumi mai tsaron gidan Djordje Petrovic bayan ya ceci bugun daga kai sai mai tsaron gida Chelsea ta lashe wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin Carabao. 19/12/23 AP - Kirsty Wigglesworth
Talla

Newcastle ta ja ragamar wasan da kwallon da ta ci tun a mintuna 16 da soma wasa ta hannun dan wasanta Callum Wilson, ana daf da Karkare wasa ne a mintuna na 90 ne  Mykhailo Mudryk ya ramawa Chelsea aka tashi wasa 1-1, akaje bugun finareti Blues din ta yi nasara.

Mai tsaron ragar Chelsea Djordje Petrovic ya ceci kungiyar wajen tare bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kungiyar ta Mauricio Pochettino za ta hadu da Fulham wacce ta doke Everton a bugun fenariti.

Yayin da Middles-brough da ta samu nasara a kan Port Vale da ci 3-0 za ta jira wadda za ta yi nasara a wasan da za’a fafata yau tsakanin Liverpool da West Ham United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.