Isa ga babban shafi

Dani Alves zai gurfana gaban kotu a watan Fabrairu bisa laifin fyade

Tsohon dan wasan Brazil, Dani Alves, zai fuskanci shari’ar zargin cin zarafin wata mata da ta ce ya yi mata a wani gidan rawa da ke Barcelona cikin watan Disanban 2022.

Tsohon dan wasan Barcelona da Brazil, Dani Alves kenan.
Tsohon dan wasan Barcelona da Brazil, Dani Alves kenan. AFP - ULISES RUIZ
Talla

Masu shigar da kara a Spain, sun bukaci adaure tsohonn dan wasan na Barcelona tsawon shekaru tara a gidan yari, wanda ke tsare a gidan yarin Spain tun lokaccin da aka cafke shi a watan Janairu, inda aka bukaci ya biya matar diyyar Yuro 150,000.

Dan fitaccen dan wasan mai shekaru 40, ya dage kan cewa babu wani ab una ci zarafi da ya taba hada shi da wannan mata.

A wata hira da aka taba yi da shi ta gidan talibijin din kasar ta Spain ranar 2 ga Janairu, Dani Alves ya bayyana cewa be taba sanin wannan matar ba, vayan da aka samu labarin ta kai karar sa ofishin ‘yan sanda.

Sai dai daga bisani Alves ya musanta wadannan kalamai nasa, yana mai cewa ya kaucewa maganar ne ddomin tsoron kada matarsa ta rabu da shi, sakamakon alakarsa da matar.

Za a saurari wannan shari’a ne a Barcelona, kamar yadda sanarwar kotun ta tabbatar.

A dokar Spain da aka yiwa gyaran fuska a bara, idan har aka samu mutum da laifin cin zarafin fyade, to kuwa zai fuskanci hukuncin zaman shekaru 15 a giddan yari.

Lokacin da wannan labari ya faru, Alves na hutu a Barcelona, bayan wasan da ya wakilci kasarsa ta Brazil a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Qatar.

Bayan cafke sshi ne, kungiyar da yake takawa leda ta Pumas UNAM ta raba gari da shi.

A lokaccin da yake kan ganiyarsa a dduniya tamola, Alves ya ci kofuna 42, da ssuka hadda da kofin gasar zakarun Turai tare da Barcelona, sai kuma Copa America sau biyu ga kasarsa Brazil.

A shekarar 2022, ya kasance dan wasa mafi tsufa da ya sshiga tawagar da ssuka wakilci Brazil a gassar ccin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.