Karon farko tawagar Burkina Faso ta samu nasara a wasan farko na gasar AFCON
Kwallon da Bertrand Traore ya jefa a ragar Mauritania a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 95, ta bai wa tawagar Burkina Faso nasara a wasan farko da tawagar ta yi a rukunin D.
Wallafawa ranar:
Wannan ne dai karo na farko da tawagar Burkina Faso ta samu nasara a wasan farko cikin yunkuri 13, a gasar lashe kofin Afrika.
Burkina Faso ce ta mamaye wasan, duk da cewa Mauritania ta samu damarmaki amma kuma ta gasa jefa koda kwallo guda.
Da wannan nasara ta Burkina Faso, a yanzu ita ke jagorantar rukunin D da maki 3, ganin yadda Algeria da Angola su ka tashi 1-1.
A cikin gasar AFCON biyar da aka yi a baya bayan nan, sau uku tawagar Burkina Faso na kai wa wasan kusa dana karshe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu