Isa ga babban shafi
AFCON

Abubuwan da ya kamata ku sani game da wasan Najeriya da Ivory Coast

An jima kadan ake shirin fafatawa a wasa mafi jan hankali karkashin gasar cin kofin Afrika ta AFCON da ke ci gaba da gudana a Ivory Coast, wasan da zai kunshi tawagar Super Eagles ta Najeriya da Elephants ta Ivory Coast mai masaukin baki, wasan da zai gudana da misalin karfe 6 agogon GMT.

Wani wasan kasashen biyu na Najeriya da Ivory Coast a shekarar 2013.
Wani wasan kasashen biyu na Najeriya da Ivory Coast a shekarar 2013. AFP PHOTO / ALEXANDER JOE
Talla

Wasan wanda zai gudana a filin wasa na Alassane Ouattara da ke birnin Abidjan, mai cin ‘yan kallo dubu 60, shi ne wasa na biyu da kowacce za ta doka a wannan gasa dai dai lokacin da Ivory Coast ke jagorancin rukunin A Najeriya kuma ke matsayin ta 3.

Daga shekarar 2006 zuwa yanzu Ivory Coast da Najeriya sun hadu sau 7 ne a gasar kasa da kasa inda Elephant ta yi nasara sau 4 Super Eagles kuma sau 3 kuma a jumlace kowaccensu ta zura kwallaye 7 ne a ragar dayarta.

Sau biyu suna haduwa a wasan sada zumunta wanda kowacce ta yi nasara a guda daya, haka zalika sun hadu a gasar zakarun Afrika, shi ma dai kowacce ta yi nasara ne sau 1, ko da ya ke Elephants ta Ivory Coast na da tarihin doke Super Eagles ta Najeriya sau 2 a gasar cin kofin Afrika yayinda Najeriyar ta yi nasara kanta sau 1.

Ivory Coast ta lashe dukkanin wasa biyu da ta taba karbar bakoncin Najeriya a gidanta, yayinda Najeriya ke da tarihin nasara kan Elephants din sau 3 a filayen wasan da bana kasashen biyu ba.

Sai dai abin dubawar shi ne, cikin wasanni 5 na baya-bayan nan da Ivory Coast ta doka, ta  yi nasara a guda 3 ta yi canjaras a 1 ta kuma sha kaye a 1, yayinda a bangaren Super Eagles ta Najeriya cikin nata wasanni biyar din na baya-bayan nan bata yi nasara a ko guda ba, sai dai ta yi canjaras a 3 yayinda ta sha kaye a 2.

Rashin nasarar Najeriya a haduwar ta yau zai haddasa mata babbar matsalar gaza iya ci gaba da kasancewa a gasar duk da kasancewar kasar a sahun wadanda ake sawa ran iya lashe kofin a wannan karon.

Ku latsa alamar sauti domin jin tattaunawa ta musamman da muka yi da Patrick Pascal , jami'in gudanarwar tawagar Super Eagles ta Najeriya........

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.