Isa ga babban shafi

Masar ta tsallaka zagayen gasar AFCON na biyu da kyar

Masar ta samu nasarar tsallaka wa zagayen gasar cin kasashen ta Afirka na biyu kuma na siri daya kwale, bayan da a fafatawarta ta daren ranar Litinin da Cape Verde suka tashi 2-2.

'Yan wasan Masar yayin murnar kwallo ta biyu da takwaransu Mostafa Mohamed ya zura a ragar Cape Verde yayin wasan karshe na rukunin B a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka da aka yi a filin wasa na Felix Houphouet Boigny da ke birnin Abidjan, Ivory Coast. 22 ga Janairu, 2024.
'Yan wasan Masar yayin murnar kwallo ta biyu da takwaransu Mostafa Mohamed ya zura a ragar Cape Verde yayin wasan karshe na rukunin B a gasar cin kofin kasashen nahiyar Afirka da aka yi a filin wasa na Felix Houphouet Boigny da ke birnin Abidjan, Ivory Coast. 22 ga Janairu, 2024. AP - Themba Hadebe
Talla

Hakan na nufin Masar kenan ta yi kunnen doki ne a dukkanin wasanni uku da ta buga a matakin rukuninta na biyu, inda ta samu maki uku.

Kunnen dokin 2-2 da aka yi tsakanin Ghana da Mozambique a dai rukunin na biyu ne daren ranar ta Litinin ya bai wa Masar din damar tsallaka wa zagayen na gaba, duk da cewar maki uku kacal ta samu.

Bayan kammala wasan rukunin na B, Cape Verde wadda tuni ta kai zagayen na siri daya kwale ke jagoranci rukunin da maki 7, sai Masar mai maki 3, yayin da Ghana ke da 2, Mozambique ma na da biyu a matsayin ta karshe.

Ba dai lallai bane Ghana ta samu damar tsallaka wa zagayen gaba saboda karancin makin da take da shi, la’akari da cewar za a zabo kasashe 4 da suka kare matakin wasannin rukuni a matsayi na uku, inda daga cikinsu za a zabi wanda ya fi yawan maki domin haduwa da sauran kasashen da suka kai zagayen ‘yan sha shidan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.