Isa ga babban shafi
AFCON

Abubuwan da ya kamata ku sani game da haduwar Ivory Coast da Senegal

A wasannin gasar cin kofin Afrika da ke ci gaba da gudana, cikin daren yau Litinin ne za a kara tsakanin Ivory Coast mai masaukin baki da Senegal mai rike da kambun gasar ta AFCON, wasan da ake kallo a matsayin haduwar manyan giwaye 2.

'Yan wasan tawagar kwallon kafar Senegal.
'Yan wasan tawagar kwallon kafar Senegal. © AFP / ISSOUF SANOGO
Talla

A haduwa 3 ta baya-bayan nan tsakanin Senegal da Ivory Coast, mai masaukin bakin ce ta yi nasara a haduwa 2 yayinda Teranga Lions ta yi nasara a guda.

A jumlace cikin wasanni 5 na baya-bayan nan da kowacce ta doka ya nuna cewa Senegal ta yi nasara a wasanni 4 tare da canjaras a wasa guda, yayinda Ivory Coast ta yi nasara a wasanni 3 ta sha kaye a 2.

Haka zalika a jerin wasannin da aka doka karkashin gasar ta AFCON, Senegal ta zura kwallaye 7 da suka kunshi 2 daga Lamine Camara kana Pape Gueye da Sadio Mane Habib Diallo da Isma’ila Sarr baya ga Abdoulaye Seck wadanda dukkaninsu suka zura kwallo guda-guda.

Dukkanin masu zura kwallo na Senegal sun taka rawar gani da ya baiwa tawagar nasarar zama mafi yawan maki a matakin rukuni na gasar, sabanin Ivory Coast wadda Seko Fofana da Krasso ne kadai suka iya zura kwallo guda-guda a gasar.

Idan aka yi duba ga matakin kasashe a jadawalin FIFA Senegal na matsayin ta 2 ne a Afrika kuma ta 20 a duniya, yayinda Ivory Coast ke matsayin ta 9 a Afrika kuma ta 52 a matakin duniya.

Senegal dai ba ta yi rashin nasara a koda wasa guda tun bayan faro gasar ba, yayinda Ivory Coast ta sha da kyar wajen samun gurbi a matakin 'yan 16 na gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.