City da Madrid sun haye zagayen kwata final na gasar zakarun Turai
Manchester City da Real Madrid sun kai zagayen dab da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai bayan wasannin da suka doka daren Laraba.
Wallafawa ranar:
Manchester City dai ta yi abin da ta saba bayan doke Copenhagen da kwallaye 3 da 1 kwatankwacin yadda ta yi mata a haduwarsu ta farko wanda ke nuna a jumlace bangarorin biyu sun tashi wasa 6 da 2. Nasarar ta City a wasan na Laraba dai za a iya cewa ba abin mamaki ba ne lura da irin bajintar da tawagar ta Pep Guardiola ke nunawa a Lig din gida da waje.
Kafa tarihi
Haka zalika nasarar ta City ya bata damar kafa tarihin kasancewa tawaga ta farko daga Ingila wadda ta doka wasanni 10 jere a gasar ta zakarun Turai ba tare da an doketa ba.
City wadda ta doka wasan na daren Laraba ba tare da ‘yan wasanta 7 da ta yi amfani da su wajen doke Manchester United a karshen mako ba, yanzu haka tan a shiryawa haduwarta da Liverpool ne a karshen wannan mako, wasan da zai fayyace kungiyar da z ata ci gaba da jagorancin teburin firimiya.
Madrid
Real Madrid ta haye ne sakamakon canjaras 1 da 1 da ta yi a haduwarta da RB Leipzig, wasan da shima ya matukar daukar hankali lura da yadda Leipzig din ta baiwa Madrid wahala a haduwarsu.
Kai tsaye Madrid ta tsallake zuwa mataki na gaba, kuma sai a ranar Juma’a ne UEFA za ta fitar da jadawalin yadda haduwar ta gaba za ta kaya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu