Al Nassr ta Ronaldo ta fice daga gasar cin kofin zakarun Asiya
Ronaldo da tawagarsa ta Al Nassr sun fice daga gasar zakarun Asia.Duk da cewa Cristiano Ronaldo ya zura kwallo a karin lokaci amma kungiyar Al Nassr ta fice daga gasar cin kofin zakarun nahiyar Asiya sakamakon kashi da ta sha a hannun Al Ain a bugun fanariti ranar Litinin.
Wallafawa ranar:
Dan kasar Portugal mai shekaru 39, shi ne dan wasan Al Nassr daya tilo da ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, yayin da tawagarsa ta Saudiyya ta tashi 3-1 a bugun fenareti, bayan 4 da 4 a wasan gida da waje.
Wannan dare ne mai cike da takaici ga tsohon dan wasan gaban na Manchester United da Real Madrid.
Haduwar farko an doke Al Nasr da 1-0 a Hadaddiyar Daular Larabawa, a wasan na daren Litinin kuwa a mintuna na 118 Ronaldo ya farke kwallo aka tashi wasa Al Nasr na ci 4-3, abin da ya kai aka tafi bugun finareti, kuma ‘yan tawagarsa biyu suka barar sai shi kadai ya ci aka karkare 3 -1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu