Isa ga babban shafi

‘Yan ta’adda sun yi barazanar kai hare-hare yayin gasar Zakarun Turai

Kungiyar ‘yan ta’adda ISIS ta yi barazanar kai wasu hare-hare filayen wasanni 4 a wasannin dab da na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai.

Filin wasan Kungiyar Real madrid na Santiago Bernabeu
Filin wasan Kungiyar Real madrid na Santiago Bernabeu REUTERS - SUSANA VERA
Talla

Wata kafar yada labarai Al Azaim Foundation da ke da alhakin yada sakonnin kungiyar, ita ce ta tabbatar da hakan a ranar Talata.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan kafar yada labaran Sarh al-Khilafah da ke da alaka da kungiyar ISIS ta bayyana shirinsu na kai wa magoya bayanta hari a filin wasa na Allianz Arena da ke Munich domin kallon wasan Bayern Munich da Borussia Dortmund.

An shirya buga wasannin ne a ranakun Talata (Yau) da Larabar makon nan.

A daren Talatar ne dai kungiyar Arsenal zata karbi bakuncin Bayern Munich, a birnin Madrid na kasar Spain.

Yayin da a washegari Laraba kuma kungiyar PSG zata ziyarci Barcelona a Faransa, yayin da Atletico Madrid kuma zata karbi bakuncin Borussia Dortmund.

Yanzu haka dai gwamnatin Kasar Spain ta tsaurara matakan tsaro gabanin wasan da za fafata tsakanin Manchester City da Real Madrid a gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.