Isa ga babban shafi

Benzema ya koma tsohon klob ɗinsa Real Madrid daga Al Ittihad domin jinya

Dan wasan gaba na Al Ittihad, Karim Benzema, ya koma filin atisayen Real Madrid.

Dan wasan Al Ittihad na Saudiya, Karim Benzema, 12/12/23
Dan wasan Al Ittihad na Saudiya, Karim Benzema, 12/12/23 AP - Manu Fernandez
Talla

Masanin harkokin wasannin kwallon kafar nan Fabrizio Romano wanda ya tabbatar da hakan a daren Laraba, ya ce Benzema ya je can ne domin a yi masa karin gwaje-gwaje da kuma jinya kan sabon raunin da ya samu.

Itama ƙungiyar Al Ittihad ta ƙasar Saudiya ta tabbatar haka, tare da mika godiya ga Real Madrid saboda taimakon da suka bayar wajen jinyar Benzema.

A wani mataki na bazata ne Karim Benzema ya bar Real ne ya koma Al Ittihad kyauta a bazara.

Wasan ƙarshe da Karim Benzema ya dokawa Real Madrid, 16/10/2022
Wasan ƙarshe da Karim Benzema ya dokawa Real Madrid, 16/10/2022 REUTERS - JUAN MEDINA

Kulob din na Saudiyya na sa ran dan wasan na Faransa ya iya buga wasanni biyar da suka rage a kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.