Isa ga babban shafi

Dan wasa Pogba zai fara haska wa a shirin fim da za a saki nan bada jimawa ba

Dan wasan kasar Faransa Paul Pogba zai haska a wani shirin fim na Faransa da za a saki a watan Afrilun shekara mai zuwa ta 2025.

Le footballeur Paul Pogba (Juventus), lors du match contre Milan, le 26 avril 2023. (Image d'illustration)
Le footballeur Paul Pogba (Juventus), lors du match contre Milan, le 26 avril 2023. (Image d'illustration) © Spada/LaPresse via AP
Talla

Tun a watan Fabrairu ne aka dakatar da Dan-wasan har tsawon shekaru hudu bisa samunsa da laifin yin amfani da kwayoyi masu kara kuzari, a yayin wasa.

Tun bayan da Dan wasan ya lashe gasar cin kofin duniya ta 2018 ne, aka fito da batun zarginsa da yin ta’ammali da miyagun kwayoyin.

Dan wasan tsakiyar tawagar kwallon kafar Faransa Paul Pogba bayan lashe kofin Duniya a Rasha.
Dan wasan tsakiyar tawagar kwallon kafar Faransa Paul Pogba bayan lashe kofin Duniya a Rasha. AFP/ FRANCK FIFE

Tun a wancan lokacin dai Dan wasan ya musanta batun, inda yace bai taba shan kwayoyi da gangan ba, don haka zai daukaka kara kan hukuncin.

Fim din wanda aka yiwa la’kabi da 4 Zéros, ci gaban wani Film ne mai suna 3 Zéros, wanda aka saki a shekarar 2002.

Dan wasa Paul Pogba
Dan wasa Paul Pogba © France 24

Rahotanni sun ce Pogba mai shekaru 31, a cikin fim din, ya taka rawa ne a matsayin mai horas da wata kungiyar ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.