Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Muradun MDG a Nahiyar Afrika

Wallafawa ranar:

Samar da ilimi ga daukacin yaran da suka kai shekarun shiga makaranta, yana daya daga cikin muradun karni da kasashen duniya 193 da ke Majalisar Dinkin Duniya suka amince, yayin babban taro duniya na karni da aka yi cikin shekara ta 2000.

WAni yaro dauke da takarda mai zanen taswirar Afrika
WAni yaro dauke da takarda mai zanen taswirar Afrika MDG
Talla

Wadannan kudirori takwas sun hada da kawar da tsananin talauci, da samar da ilimi na bai daya, da daidaiton jinsi, domin bunkasa rayuwar mata da rage mutuwan mata wajen haihuwa da bunkasa kiwon lafiyar mata, da magance illar cuta mai karya garkuwar jiki da zazzabin cizon sauro, tare da kare muhalli sannan na karshe hadin gwiwa domin samun ci gaba.

Shekaru kusan 10 bayan amincewa da kudirorin kuma shekaru biyar kafin cikar wa’adin da aka tsara na shekara ta 2015, kasashe masu tasowa na ci gaba da fafutukar cim ma kudirin.

Amma yanzu Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan yadda kasashen Afrika suka zama na baya ga dangi wajen rashin tabuka abun kirki idan aka kwatanta da kasashen Asiya da Latin Amurka.

A cikin Shirin zaku ji tsokacin dam asana suka yi dangane da dalilan da ke tarnaki wajen cim ma wannan burin a kasashen Afrika.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.