Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Yakin Mali ya zo matakin karshe, inji Hollande

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa yakin da ake gwabzawa a kasar Mali ya zo matakin karshe, tare da jinjinawa namijin kokarin da dakarun kasar Chadi suka yi a sakamakon wani gagarumin farmaki da yayi sanadiyar hasarar rayuka masu yawa daga bangaren ‘Yan ta’adda.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande a lokacin da ya ziyarci kasar Mali
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande a lokacin da ya ziyarci kasar Mali Reuters/Joe Penney
Talla

Hollande dai ya kara bayyana cewa dakarun Faransa sun mai da himma a yakin wanda aka gwabza shi a tsaunukan Ifoghas. 

“Dakarunmu sun maida himma a yakin. Domin yanki ne da ake kira da tsaunukan Ifoghas, inda muke tunanin cewa mayakan jahadin yan ta’adda masu yawan gaske sun yi hijira ko sun boye.”

A cewar Hollande abukanmu dakarun Faransa, wato ‘Yan Chadi sun kai gaggarumin farmaki da ya yi muni, wanda ya haifar da hasarar rayuka masu yawa, inda ya sake jinjinawa namijin kokarin da dakarun na Chadi suka nuna a yakin.

Shugaban na Faransa ya bayyana wannan kokari na nuna irin zumuncin da kasashen Afrika ke nunawa ga kasar ta Mali.

“Wannan fada zai ci gaba, kuma a hakikanin gaskiya zai iya zama daya daga cikin matakin karshe na yakin, domin kuwa babu shakka a cikin wadannan tsaunuka ne yan ta’addan suka taru ko kuma suka boye.”
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.