Isa ga babban shafi
Syria

Taron kawayen kasar Syria ya jaddada aniyar ba da taimako ga ‘Yan tawaye kasar

Taron da kawayen kasar Syria da suka hada da kasar Amurka da kasashen Turai da na Larabawa suka gudanar, ya fitar da sanarwar cewa kasashen za su cigaba da taimakawa kungiyar hadaka ta ‘Yan tawayen Syria da ke fafatawa da shugaba Bashar al – Assad.

Taron kawayen kasar Syria
Taron kawayen kasar Syria
Talla

“Ministocin kasashen sun jaddada cigaba da taimakawa kungiyar hadaka ta ‘Yan tawayen kasar Syria ta fuskar siyasa da kayayyaki, domin sune ainihin wakilan al’umar kasar.” Wata rubutacciyar sanarwa da ta fito daga kasar Italiya ta bayyana bayan kammala taron da aka yi a birnin Rome.

Taron dai ya samu halartar kasashen 11 da kuma wakilan kungiyar hadaka ta ‘Yan tawayen kasar ta Syria.

Sanarwar ta kuma nuna muhimmancin kawo daidaituwa ta fuskar siyasa a kasar, inda ta kuma bayyana shirin ci gaba da taimakawa ‘Yan tawayen musamman ta hanyar da za su kare kansu.

Taron har ila yau ya nuna damuwarsa ga irin halin da fararen hula su ka shiga a kasar, inda ya yi kira ga gwamnatin Assad da ta bar kai hare-hare kan yankunan da fararen hula ke zaune.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.