Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Barcelona ta sake shan kayi a hanun Real Madrid da ci 2-1

Barcelona ta sake shan kayi a hanun Real Madrid da ci 2-1 a fagen Gasar La Liga wannan kuma shine karo na biyu da Madrid ke doke Barcelona a cikin kwanaki biyar a karawar da suka yi. A daya bangaren kuma mai horar da ‘yan wasan Athletico Madrid, Diego Simeone, ya nuna rashin jin dadinsa bayan ‘yan wasan nasa sun ta shi canjaras da Malaga.  

Dan wasan Barcelona Lionel Messi
Dan wasan Barcelona Lionel Messi REUTERS/Ricardo Ordonez
Talla

Kuma da har Atheltco Madrid ta yi amfani da shan kayin da Barcelona ta yi a hanun Real Madrid a ranar Asabar, da hakan ya basu damar rage tazarar maki 9 da aka basu a gasar.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar ta La Liga na nuna cewa, Espanyol sun tashi canjaras da Valladolid, kana Deportivo La coruna da Vallecano suma suka tashi canjaras, yayin da Atheletico Bilbao ta bi Osasuna har gida ta lallasa tad a ci 1 mai ban haushi.

A yanzu haka Barcelona ce ke gaba da maki 68 a gasar, kana Athletico Madrid na biye da ita da maki 57, yayin da Real Madrid ke matsayi na uku da maki 55.

A yau Litinin Sevilla da Celta Vigo zasu fafata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.