Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Real Madrid ta mamayi Mallorca da ci 5-2, Barcelona ta doke Rayo da ci 3-1

A cigaba da gasar La Liga, Barcelona ta doke Rayo Vallecano da ci 3-1, Lionel Messi ne kuma ya zira kwallaye biyu a wasan a yayin da Villa ya zira kwallo daya. Valencia a daya bangaren ta doke Real Betis da ci 3-0, sannan Real Madrid kuwa ta lallasa Mallorca da ci 5-2,kuma Cristiano Ronaldo na daya daga cikin ‘yan wasan da suka zira kwallaye, a yayin da Getafe ta doke Athletico Bilbao da ci daya mai ban haushi, kana Real Sociedad ta doke Valladolid da ci 4-1.  

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo
Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

A yanzu haka Barcelona ce dai ke cigaba da baza sarautarta a saman teburin gasar da maki 74 inda ta ba Real Madrid wacce ke da maki 61 tazarar maki 13 a matsayi na biyu.
Ita kuwa Athletico Madrid na jeri na uku da maki 60, inda kuma Real sociedad ke biye da ita da maki 47 a matsayi na hudu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.