Isa ga babban shafi
FIFA

Brazil a shirye ta ke ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya - Blatter

Hukumar kwallon kafar duniya ta FIFA, ta kebe ran 6 ga watan Disambar wannan shekara a matsayin ranar da za a kasafta kungiyoyin kwallon kafar kasashen duniya a cikin rukunansu, domin karawa a gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa. 

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter REUTERS/Stringer
Talla

Shugaban hukumar ta FIFA, Sepp Blatter ne ya bayyana hakan, inda ya ce za a yi taron zaben kasafta kasashen ne a Jihar Bahia dake kasar ta Brazil.

Haka zalika, Blatter ya kore rade-radin da ake yi dake cewa kasar ta Brazil na samun cikas wajen kammala shirye-shireynta na daukan bakuncin gasar.

Ya kuma kara da cewa ire-ire kalubalan da kasar ke fuskanta game da shirye shiryen, abu ne da kan faruwa ga duk wata kasa da za ta dauki bakuncin gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.