Isa ga babban shafi
Amurka-Iran-Isra'ila

Ziyarar Obama a Gabas Ta Tsakiya

Shugabannin Yahudawa sun tarbi Obama hannu biyu tare da yaba ma sa wajen kare muradun Isra’ila a wata ziyarar farko da ya kai yankin Gabas ta tsakiya a matsayin shugaban kasar Amurka. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da shugaban Yahudawa Shimon Peres ne suka tarbi Obama.  

Shugaban Amurka Barack Obama tare da Shugabannin Yahudawa a filin saukar jirgi na birnin Kudus
Shugaban Amurka Barack Obama tare da Shugabannin Yahudawa a filin saukar jirgi na birnin Kudus AFP/Jack Guez
Talla

A lokacin da ya ke jawabin karbar bakuncin Obama, Netanyahu ya godewa shugaban akan tsayawa tsayin daka wajen kare martabar Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.

Shugaba Peres mai shekaru 89 ya ce Amurka ta taka rawa wajen kare martabar Isra’ila don haka suna mika godiya ga Barack Obama.

Shugaba Obama ya ce kawancen Isra’ila da Amurka na har abada ne amma yace Amurka tana fatar Isra’ila za ta zauna cikin kwanciyar hankali da makwabtanta.

Shugaba Peres ya shaidawa Obama fatar samun zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falesdinawa.

Obama yace sasanta rikicin Isra’ila da Falesdiniwa baya cikin agendar ziyarar shi amma shugaban ya ce ya kawo ziyara ne domin ganawa da sabuwar gwamnatin Isra’ila da Falesdinawa, lamarin da ya jefa alamar tambaya ga Masana game da dalilin ziyarar ta Obama.

Amma wasu suna ganin Obama yana ziyara Isra’ila ne domin ya tabbatar wa kasashen Larabawa karfin kawancen da ke tsakanin Amurka da Isra’ila.

Rikicin Nukiliyar Iran da yakin Syria suna cikin batutuwan da Obama zai tattauna da shugabannin Yahudawa.

A baya Netanyahu ya yi gargadin Iran tana gab da kammala shirinta na mallakar Makamin Nukiliya amma Obama yace za’a kwashe tsawon shekara kafin Iran ta cim ma kudirinta.

Akan haka ne masana suke ganin batun Nukiliyar Iran ne babban dalilin ziyarar Obama a Isra’ila.

Amma shugaban Falesdinawa Mahmud Abbas yace yana fatar Obama zai shiga tsakaninsu da Isra’ila domin sakin Falesdinawan da Isra’ila ke tsare da su a gidan yari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.