Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Brazil 2014: Najeriya za ta kara da Kenya, Nijar da Burkina Faso a wasannin share fage

A karshen makon nan mai zuwa ne za a cigaba da share fagen shiga gasar cin kofin duniya, wanda Brazil za ta dauki bakuncinshi a shekara mai zuwa. A Nahiyar Afrika, Afrika ta Kudu wacce ke da maki biyu a rukunin “A”, za ta kara da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Ethiopia ko kuma Habasha ce dai ke saman teburin wannan rukunin da maki 4, za kuma ta kara ne da Botswana. 

Dan wasan Kenya da na Najeriya a wata karawa da suka yi
Dan wasan Kenya da na Najeriya a wata karawa da suka yi images.supersport.com
Talla

A rukunin “B” kuma Tunisia wacce ke saman rukunin da maki 6 za ta kara ne da Sierra Leone, a yayin da Cote d’ I Voire za ta fafata da Gambia.

Jamhuriyar Nijar kuma za ta kaiwa Burkina Faso ziyara ne a Ouagadougou, a dai dai lokacin da Najeriya za ta kara da Kenya a birnin Calabar, kuma ita ke saman rukuninsu na “F” da maki 4.

Mozambique kuwa za ta kara ne da Guinea, kana Namibia ta kara da Malawi, a yayin da Equatorial Guinea za ta fafata da Cape Verde.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.