Libya ta nemi hurumin daukar nauyin gasar Afrika a 2017
Kasar Libya ta fara tura bukatar ta zuwa ga hukumar Kwallon Afrika CAF domin karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika a 2017. Bayan an ba Afrika ta kudu huruminta na daukar nauyin gasar a a bana.
Wallafawa ranar:
Kasar Libya ce dai ya kamata ta dauki gasar cin kofin Afrika da aka kammala a bana a kasar Afrika ta kudu amma saboda rikicin kasar da ya yi sanadiyar kawo karshen mulkin Kanal Gaddafi aka ba kasar Afrika ta kudu damar daukar nauyin gasar.
Mataimakin Firimiyn Libya Awad al-Baraassi, ya ce suna fatar daukar nauyin gudanar gasar domin wasannin su zo dai dai da lokacin bukin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu