Isa ga babban shafi
Afghanistan-NATO

Kungiyar Taliban za ta ci gaba da ta da kayar ba bayan janyewar sojin kawance, inji Amurka

Tsohon kwamandan kungiyar Tsaro ta NATO, Janar John Allen da ya bar kasar tun watan Febrairun da ta gabata ya ce hare-hare da kungiyar Taliban ke kaiwa a kasar Afghanistan zai cigaba ko da bayan dakarun na NATO sun fice daga kasar. 

John Allen
John Allen REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Allen ya yi wannan bayani ne a jawabin sa a birnin Washington da ke kasar Amurka ,inda ya jaddada cewar hare haren da ‘yan Taliban ke kai wa zai cigaba,

Tsohon shugaban ya cigaba da cewa bajintarsu ta zarce tunani inda daga karshe ya tabbatar da cewa akwai aiki ja nan gaba a kasar mussaman wajen ganin an tabbatar dakarun kasar ta Afghanistan sun tsaya da kafarsu.

Sojojin kawacen za su janye ne daga kasar ta Afghanistan watan Disambar a shekarar 2014.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.