Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Chelsea ta fitar da Man U a gasar FA Cup

Manchester United ta fice daga gasar FA Cup bayan ta sake karawa tsakaninta da kungiyar kwallon kafar Chelsea a gasar ta FA Cup, inda aka tashi a wasan da ci 1-0. Dan asalin kasar Senegal Demba Ba ne ya zirawa Chelsea kwallonta jim kadan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, wacce itake rike da kofin gasar.  

'Yan wasan Chelsea na murnar samun nasara akan Man U
'Yan wasan Chelsea na murnar samun nasara akan Man U
Talla

Yanzu haka Chelsea ta tsallaka zuwa zagayen daf da na karshe inda za ta kara da abokiyar hamayyarar Manchester United a cikin gida, wato Manchester City, a ranar 14 ga watan nan na Aprilu.

Wannan sakamakon wasa ya sake kashe burin Manchester United na lashe kofin gasar na FA Cup, bayan ta fice daga gasar Champions League.

Sai dai akwai yiwuwar ita ce za ta lashe kofin gasar Premier League ganin cewa itake saman teburin gasar da maki 77 a yayin da Chelsea ke matsayi na hudu da maki 55.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.