Isa ga babban shafi
Syria

Turkiya da Jordan na nuna shakku kan yin amfani da karfin soji a Syria

Kasashen dake makwabtaka da kasar Syria na nuna jan kafa kan yunkurin Amurka na amfani da karfin soji, idan an tabbatar da Gwamnatin kasar ta yi amfani da makami mai guba.

Talla

Kasashen Turkiya da Jordan wadanda ke adawa da shugaba Bashar al assad, na fargabar cewar daukar duk wani matakin soji na iya haifar da matsala a cikin kasashen su.

Wata majiya dake kusa da Gwamnatin Turkiya ta nuna shakku kan duk wani rahota da ya shafi amfani da makamin kare dangi ko kuma makami mai guba, inda suke cewar haka aka yi a Iraqi kana aka yi nadama akai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.