Isa ga babban shafi
Syria

MDD da Rasha sun amince da matakan kawo karshen rikicin Syria

Gwamnatin kasar Rasha tare da Sakateren Majalisar Dinkin Duniya sun amince da matakin gaggauta gudanar da taro domin tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin kasar Syria. A wata ganawa da Ministan harakokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya yi da sakateren MDD Ban Ki-moon, Mista Lavrov ya ce akwai bukatar a gaggauta gudanar da taro domin tattauna makomar Syria.  

Janar Sakataren MDD, Ban Ki-moon (hagu) da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin (Hagu)
Janar Sakataren MDD, Ban Ki-moon (hagu) da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin (Hagu) 4.bp.blogspot.com
Talla

A nasa Bangaren, Ban Ki-moon ya yi kira ga gwamnatin Syria ta amince da wakilan MDD su shiga kasar domin gudanar da bincike game da zargin da ake wa kasar na amfani da makamai masu guba.

Wannan dai na zuwa ne bayan Shugaban Amurka Barack Obama da Firaministan Turkiya sun ce babu wata hanya ta kawo karshen rikici Syria illa shugaba Bashar Assad ya yi murabus.

Tuni kuma Shugaban Faransa Francois Hollande ya nemi kasashen Duniya su shawo kan Syria domin kawo karshen Bashar Assad a kasar.

A watan Yuni ne dai ake sa ran Manyan kasashen Duniya za su gana game da daukar mataki akan Syria bayan sun kasa cimma aiwatar da komai a irin wannan taron da suka gudanar a bara.

Kasar Rasha dai ta ce akwai bukatar a tuntubi gwamnatocin kasashen Iran da Saudia game da warware rikicin na Syria wanda ya lakume rayukan sama da mutane 70,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.