Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta jima da kafa na’urorin sarrafa makamin nukiliya- IAEA

Iran ta jima da kafa wasu na’urorin da ke sarrafa makamashin Nukliya a tasharta da ke garin Natanz, tsakanin watanni 3 da suka wuce, kamar yadda hukumar makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya na IAEA ta ce.

Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad
Shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmedinejad (Photo : AFP)
Talla

Iuzwa ranar 15 ga watan Mayu, akalla wasu na’urorin tace makamashin nukiluya hudu ne aka kafa sannan kuma da wasu shirye shirye da aka gudanar domin tace makamashin Uranium.

Shi dai wannan shiri na nukiliyar kasar Iran ya kasance wani abin damuwa ga kasashen duniya, inda suke zargin kasar da cewa tana da niyyar kera makaman nukiliya ne.

Rahotanni dai na nuni da cewa yanzu haka Iran na shirin kafa wasu na’urorin tace makamashin nukiliyya na zamani har guda dubu uku a wannan tasha da ke Nantaz,

kuma kafin nan akwai wasu akalla dubu 12 da dari biyar da take amfani da su a wannan tasha.

A cikin wannan rahoto da hukumar ta makamashin nukiliya ta duniya ta fitar, ta ce har yanzu Iran ba ta soma yin amfani da irin wadannan na’urori a tasharta da ke garin Fardo ba.

Sai dai duk da wannan zargi da kasashen duniya ke yi ma ta, Iran ta ce shirin nuliliyarta na zaman lafiya ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.